Skip to main content

TSOKACI A KAN YANDA AKE HADA WEBSITE(1)

 


Gaba daya website ko kuma shafin internet za'a iya raba shi gida biyu ta la'akari da yanda ake hada shi (wato web design) da kuma abubuwan da ake amfani da su wajen hada shi. Hada website ko kuma web design ya kasu zuwa gida biyu kamar haka:

1. Sashen da ake iya gani idan an ziyarci website din (wato Front-end)

2. Sashen da mutum wanda ya ziyarci website din baya iya gani (wato Back-end)

1. SASHEN DA AKE GANI IDAN AN ZIYARCI WEBSITE(FRONT-END)

Shi front-end, ko kuma sashen da ake gani idan an ziyarci website, ya kunshi duk wani dubaru da ake iya amfani da su wajen yin designing ko kuma tsara duk wani abu da ke a cikin website wanda idan mutum ya shiga website din zaya iya gani. Abubuwan da za'a iya gani a cikin website sun hada da hotuna, videos, rubutu, audio da dai sauransu. Ana amfani da abubuwa biyu zuwa uku ne wajen designing din front-end na website. 

Na daya, kuma jagora daga cikin wadannan abubwa da ake hada website da su, shine HTML (Hypertext Markup Language). Shi HTML yare ne na computer (ko kuma programming language) wanda kuma shine ginshiki na ko wane irin website da ka sani, domin da shi ne ake designing din taswira, tsari ko kuma skeletal na website. Da HTML ake amfani wajen sanya rubutu, hoto, video, malatsai (buttons), wajen da mutum zaya iya sanya rubutu (wato textbox) da dai sauransu. Duk wani abu da ka sani zaka iya tabawa ko kuma aiwatar da wani abu a cikin website ta hanyar shi wannan abun, to ana amfani da HTML ne wajen sanya shi.

Baya ga HTML, abu na biyu da ake amfani da shi wajen yin design din front-end (wato sashen da mutum ke iya gani) na website shine CSS (Cascading Style Sheet). Shi CSS ana amfani da shi ne a website domin kayata website din ta hanyar sanya wasu abubuwa kamar su kaloli (colors), zane da kuma positioning (wato kuma tabbatar da cewa duk wani abu da aka sanya ta hanyar HTML to an dora shi a inda ya kamata). Ba don CSS ba, to da website bai yi kyawon da muke ganin shi da shi ba a yau, domin idan ba'a yi amfani da CSS ba wajen designing din website, to kusan komi da ke cikin wannan website zaya fito ne cikin layi guda ko kuma duk su hade a waje guda ta yanda ba zaka iya rarrabewa a tsakaninsu ba.

Daga CSS kuma, abu na uku da ake amfani da shi wajen yin designing na front-end (wato sashen website wanda mutane kan iya gani) shine JavaScript. JavaScript shima yaren computer ne (programming language) da ake amfani da shi wajen sanya website ya zama dynamic, wato website mai sauya kamannu kuma wanda ke iya amsa bukatar mutum (misali wajen yi rajista ko kuma Log in). Dynamic website shine website wanda mutum zaya iya neman wani bayani (ko kuma searching din wani bayani) kai tsaye a cikinshi kuma ya maido ma mutum da amsar wannnan bayani da ya nema. A lokaci guda kuma ta yanyar javascript, za'a iya sanya website din ya nemi ko kuma ya tambayi mutum wani bayani wanda za'a iya amfani da shi wannan bayani a cikin website din ko kuma wani abin daban. In aka so, Za'a iya design na website ba tare da javascript ba amma kuma yana da matukar amfani musamman ma idan mutum yana bukatar wannan website ya zama dynamic.

Wadannan abubuwa guda uku, wato HTML, CSS da kuma Javascript, sune ake amfani da su wajen designing ko kuma hada sashen website wanda mutane ke gani idan sun ziyarci website din (wato front-end). Mutum wanda ya san wadannan abubuwa guda ukku (HTML, CSS da Javascript) kuma yake hada website ta hanyar amfani da su, shi ake kira da FRONT-END DEVELPER wato wanda ke designing na sashen website wanda mutane ke iya gani idan suka ziyarci wannan website din.

Mafi yawancin mutane kan shiga shafukan internet (wato web pages) a ko wane lokaci, amma ko sau daya basu taba damuwa da cewa shin wai duk wadannan abubuwan da suke gani a cikin wadannan shafukan ta yaya ake hada su ne? kuma ta yaya wasu ke iya ziyara tare da ganin abin da ke website din? Shin wai bayanan da a ko da yaushe muke sanyawa kamar hotuna, videos da kuma rubutu a ina suke tafiya ne? Duk da cewa wasu mutanen sukan yi irin wadannan tambayoyi, kuma suna son su san hakan, wata kila rashin wanda zaya war-ware masu zare da abawa shine ya hana su samun wannan ilimin. Cikin wannan kasida ta 1 daga cikin jerin kasidojin da zamu rika kawo muku akna website da kuma web design, zamu tattauna ne akan shafin Internet (wato website) da kuma abubuwan da ya kunsa.

Kamar yanda mafi yawanci daga cikin masu karanta wannan kasidar suka sani cewa, Website dai wani abu ne da ke kunshe da shafuka kala-kala wadanda kuma ko wane daga cikin su yana dauke ne da wani bayani na musamman wanda dukkan wanda ya ziyarce shi zaya iya gani. Website za'a iya cewa kamar wani akwati ne ko kuma folder da ke dauke da shafuka daban-daban da aka ajiye a saman kafar SADARWA ta internet, inda mutum kan iya connecting ga wannan folder din tare da duba duk wani abu da ke a cikinta ( wato shafuka) ta hanyar ziyartar adireshin da aka baiwa ita wannan folder din (website address).

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Muhimman bayanai akan Computer Programming

  MUHIMMAN BAYANAI AKAN COMPUTER PROGRAMMING Program: Jeri ne na umarni wanda CPU ke aiwatar dashi. Za'a iya bayyana program a matsayin jerin umarni wanda aka tsara, wanda idan aka aiwatar dashi yakan sanya kwamfuta tayi abin da ake so tayi. Haka zalika computer program jerin umarni ne masu nasaba da juna waɗanda ke baiwa kwamfuta umarnin yadda zata cim ma takamaiman aiki. Wannan dalilin yasa ba tare da program ba kwamfuta ba zata iya aiwatar da komai da komai b Programming: shine aikin rubuta code ko yin aiki domin rubuta computer program. Programmer: shine wanda yake rubuta code ko jerin umarni ga kwamfuta yayin programming. Code (source code): kalma ce wadda ake amfani da ita don bayyana rubutu wanda computer programmer yake rubuta shi ta amfani da dokoki da ƙa'idoji na wani programming language. Coding: wannan shine yin rubutu ko rubuta code. Computer language: shine yaren da kwamfuta take amfani da shi domin fahimtar aikin da aka umarce ta tayi. Programming Language: shin...

Yanda Ake Koyon Programming

  YAYA AKE KOYON PROGRAMMING? A cikin wannan kasida, mun kawo muku wasu matakai da zaku bi domin koyon programming a saukake. Wadannan matakai sune kamar haka: 1. Zabar programming language 2. Farawa da kadan-kadan 3. Yin amfani da code din da wasu programmers din suka rubuta 4. Yawaita shiga dandalin programmers. 1. Zabar Programming language Sau da yawa masu koyon programming sukan rasa ko ma da wane programming language zasu fara. Wannan na faruwa saboda yawan programming languages da muke da su. Kuma a ko da yaushe ka tambayi masana akan wane programming ne yafi dacewa a fara da shi, zaka ji a ko da yaushe amsoshinsu na cin karo da juna. Wani programmer din idan ka tambaye shi sai y ace ka fara da java, a lokacin da wani zaya iya ce maka ka fara da C, shi kuma wani cewa zaya yi ka fara da swift, ko Ruby da dai makamantansu. Maganar gaskiya babu wani programming da za’a dauka a ce shine ya fi kowa ne programming saukin koyo, hasali ma dai, zaka iya fara ...