YAYA AKE KOYON PROGRAMMING?
A cikin wannan kasida, mun kawo muku wasu matakai da zaku bi domin koyon programming a saukake.
Wadannan matakai sune kamar haka:
1. Zabar programming language
2. Farawa da kadan-kadan
3. Yin amfani da code din da wasu programmers din suka rubuta
4. Yawaita shiga dandalin programmers.
1. Zabar Programming language
Sau da yawa masu koyon programming sukan rasa ko ma da wane programming language zasu fara. Wannan na faruwa saboda yawan programming languages da muke da su. Kuma a ko da yaushe ka tambayi masana akan wane programming ne yafi dacewa a fara da shi, zaka ji a ko da yaushe amsoshinsu na cin karo da juna. Wani programmer din idan ka tambaye shi sai y ace ka fara da java, a lokacin da wani zaya iya ce maka ka fara da C, shi kuma wani cewa zaya yi ka fara da swift, ko Ruby da dai makamantansu. Maganar gaskiya babu wani programming da za’a dauka a ce shine ya fi kowa ne programming saukin koyo, hasali ma dai, zaka iya fara koyon programming da ko wane language ka ga dama.
2. Farawa da kadan-kadan
Kamar yanda muka fada a kasidarmu da ta gabata, daya daga cikin kura-kuran da masu koyon programming kan tabka shine, suna tunanin cewa da sun fara koyon programming shi ke nan take zasu fara hada softwares ko application. Misali, lokacin da muke a makaranta kafin mu koyi yanda ake rubutu, farko sai da muka fara koyon haruffa da bakake, sana muka fara koyon yanda aka baki da wasali (consonants and vowels), sannan muka fara koyon yanda ake rubuta kananun kalmomi, sannan manyan kalmomi, daga kuma muka koyi yanda ake rubuta jimla (sentence). Shima programming haka yake sai ka koyi wasu ‘yan kananan abubuwa a hankali kafin a iya fara gina software ko kuma applications. Amma kuma mutum ya tabbatar da cewa duk wani sabon abu da ya koya to yayi exercise sosai a kansa ta yanda zaya zauna masa sosai.
3. Yin amfani da code din da wasu programmers din suka rubuta
Da zaran ka koyi wasu abubuwa da dama a programming, abun da ya kamata ka fara yi shine ka fara amfani da code (ko program) da wasu programmers din suka rubuta ta hanyar fahimtarsa tare da canja wasu abubuwa ya zuwa yanda kake bukata. Akwai wurare da yawa zaka iya samun free code na programmers, daya daga cikin wadannan wurare shine gihub.com. Ko wane irin programming ne kake koyo sai ka sami code dinsa a github domin shine mafi girman wuri da programmers ke sharing din code nasu.
4. Yawaita shiga dandalin programmers.
Abu na gaba kuma da ya kamata mai koyon programming ya rika yi shine yawaita shiga dandalin da programmers ke baje kolin matsalolinsu tare da taimakon juna. Akwai irin wadannan website da dama, amma mai girma daga cikinsu shine stackoverflow.com. Duk wata matsala da ka samu wajen yin programming dinka, idan ka shiga wannan waje sai ka sami wanda zaya magance maka wannan matsala nan take kuma a kyauta!
A kasidarmu da zata biyo wannan, in Allah ya yarda zamu tsokaci akan hanyar da zaka bi wajen zabar programming language da ya dace da kai, dangane da abin da zaka yi da wannan programming din.
gaskiya munajin dadin wannan karatu mai albarka allah yakara basira
ReplyDeletemun gode sosai, ALLAH ya kara fahimta
ReplyDeleteMasha Allah muna godiya
ReplyDeleteZan idan mutum Yana so yakoya ta Ina yakama yafara
ReplyDeleteMasha Allah,kana da wani group ne WhatsApp ko Facebook,Dan Allah idan akwai Inna bukata,07087412960,ga number ta
ReplyDelete