Assalamu alaikum,
Mutane da dama masu son fara koyon programming (wato yaren na'ura mai kwakwalwa) ma’ana Computer da harshen turanci, amma basu san ta inda zasu fara ba. Wasu kuma sun rasa da wanne yare ya kamata su fara. Muna fatan InshaAllahu wannan rubutun zai taimaka ma duk wanda yake fuskantar irin wannan matsala da duk ire-iren wadannan matsalolin.
Da farko shidai sanin ilimin programming language din da mutum ya kamata ya koya ya ta'allaka ne akan manufar menene mutum yake son zama ko kuma mene ne aikin da mutum yake so yayi. Bari in buga misali yanda kowa zai fahimta. Yanzu idan mutum zaije jami’a tun wajen rubuta jarabawar jamb zai yanke shawarar abinda yake so ya karanta a jami’a. To haka abun yake shima a wannan 6angaren.
Yanzu zamu dauki wasu daga cikin 6angarorin Programming sannan mu fadi programming language din da ake amfani dasu a wan nan 6angaren. Daga nan sai mutum yasan wane language ya kamata ya fara koya.
Website design and development: Wannan shine ilimin qirqirar dakuma qayatar da Websites,ya kunshi duk wasu tsare-tsare da zaka kawo a websites.Shidai wannan bangaren ya rabu zuwa gida biyu ne. Akwai ''Front-end'', wato bangaren da wanda ya ziyarci website din zai iya gani, da kuma ''Back-end'' wato bangaren da babu wanda zai iya gani sai wanda ya kirkiri manhajar. Programmig Languages din da ake amfani dasu a Front-end sune: Html 5, Css, React,Angular,JavaScript, dss... Sai kuma wadanda ake amfani dasu a Back-end sun hada da: Javascript, Php,Ruby,django,dss... . Programmers din dake Website design and development na iya zama “Front-end” ko kuma “back-end” developers.Zaka iya zaban guda daya a cikinsu ka koya ko kuma duka wanda ya’iya duka ana kiranshi da “Full-Stack developer”.
Mobile App development: Wannan shine ilimin kirkiran Application irin na waya. Misali kamarsu MX player, Xender,Opera mini,dss… A takaice dai duk Application da muke zuwa google Play Store mu dauku to su ake nufi. Akwai nau’ukan programming languages da yawa da ake amfani dasu wajen kirkiransu. Kamarsu: Flutter, Kotlin, C++, Java, Python dss... Amma programming languages din da suka fi karfi sannan kuma sanannu sune Java da Kotlin . Mafi yawancin Applications din da suke a Playstore da Java aka yisu. Amma yanzu Kotlin yazo ya wuce Java a 6angaren sanuwa da kuma sauki. Idanda ace mai karatu zai tambaya shawara ta idan zai paara mobile app developing to Ni kaina zan bashi shawarar ya ya koyi Kotlin ko Flutter ne ba Java ba, saboda Java yanada wahalan koyo sosai.
Ba a wadannan 6angarori da’aka lissafo asama ne kawai ake amfani da programming languages ba, saidai kawai wadanan kamar gabatarwa ne akan Programming languages. Akwai 6angarori da yawan gaske wanda ake amfani dasu. Amma asalin sakon da nake so na isar shine dole sai mutum yasan aikin da zaiyi da programming language kafin ya fara koyanshi, bawai hakanan mutum zaije ya fara koyanshi ba.
InshaAllah a rubutun mu nagaba zamuyi cikakken bayani akan web development.
RUBUTU DA IKON MALLAKA shafin “Koyon Programming da hausa”.
Comments
Post a Comment