Skip to main content

Yanda Zaka Rage ma Wayarka Shan Data

 



Mutane da yawa, musamman ma  masu amfani da manyan wayoyi na zamani, sukan koka akan yanda datarsu ke saurin karewa da  zarar sun yi subscription.  Wannan dalili ne ya sanya wasu ma kan bar yawan bude datar ko kuma ma su rabu da wayar baki daya. Wannan abu  ba hakanan kawai faruwa ba, akwai dalilai da kan sanya hakan. A cikin wannan kasida tamu, zamu yi tsokaci akan wadannan dalilan da kuma yanda zaku shawo kan wannan matsala ta yawan shan data.


Sanin kowa dai ne a wannan lokaci da muke a cikin, kusan dukkanin wayoyin da muke amfani da su, musamman ma manya wayoyi,  mafi yanwancin aiyukansu sun dogara ne akan internet. Wannan dalili ne ya sanya cewa, idan har mutum baya da data a cikin layinsa, to sai ka ga ya kasa yin wasu da yawa daga cikin muhimman ayyukan da wadannan wayoyin kan yi.


Saboda amfanin da wadannan wayoyin ke yi da data ne ya sanya aka basu damar cewa, da zarar mutum ya kunna data, to su ci gaba da yin wasu muhimman aiyuka ba tare da sun sanar da mai wayar ba (wato background data). Wasu wayoyin kuma application din su ne ke yin update lokaci zuwa lokaci domin inganta ko kuma sabinta yanayin yanda wayar ke aiki. Wani lokacin kuma, applications din da mutum ke yin installing a cikin wayar ne ke amfani da wannan damar domin yin wasu ayyukan da ke bukatar data ba tare da sun nemi izinin mai wayar ba.


Shin ko kana cikin wadanda ke fama da irin wannan matsala ta shan data? To kwantar da hankalinka, ga hanyoyin da zaka bi domin ragewa ko kuma tsaida wannan shan data da wayarka take yi.


Background Data


App background data shine babban abin da ke sanyawa waya ta rika shan data babu gaira babu dalili! Duk da cewa wayoyi da yawa na zuwa da wannan tsarin, wayoyin android sun fi kaurin suna akan wannan matsala. To sai dai, duk da haka, wayoyin android din suna  bada dama ga mutum domin ya zabi applications din da yake bukatar ya rika amfani da data a ko da wane lokaci, tare da kuma kange wasu application din daga yin amfani da data ba tare da saninshi ba.


Domin gane ko wane application ne yake shan data ba tare da saninka ba, to sai ka shiga cikin Settings na wayarka, ka duba daga kasa kadan, zaka ga inda aka sanya Data Usage. Idan ka shiga wurin zaka ga list na duk application da ke amfani da datarka, idan kaga akwai wani wanda baka yarda da shima to zaka iya hanashi yin amfani da data har sai ya samu izininka. Domin tsaida application daga shan data kai tsaye, sai a bi wadanna matakan:


1 .  Shiga cikin settings


2 .  Duba daga kasa kadan, akwai inda aka sanya Data Usage


3 . Idan ka shiga Data usage, zaka ga list na applications din da ke shan data da kuma yawan datar da suka sha


4 . Domin tsaida application daga shan data, sai ka taba application din, wani page zaya bude.


5 . Sai ka duba daga kasa, akwai inda aka sanya Restrict app background data, sai ka taba ko kuma ka kunna.


Haka zaka yi ma duk wani application da kake bukatar takaita yanayin shan datar da yake a wayarka. Daukar wadannan matakan kadai, zaya taimaa maga wajen rage yanayin yanda wayarka ke sha maka data sosai.


Wannan sune hanyoyi da zaka bi domin rage yawan data da wayarka she amfani da ita ba tare da saninka ba. Da fatan kun amfana da wannan kasida

Comments

Popular posts from this blog

Muhimman bayanai akan Computer Programming

  MUHIMMAN BAYANAI AKAN COMPUTER PROGRAMMING Program: Jeri ne na umarni wanda CPU ke aiwatar dashi. Za'a iya bayyana program a matsayin jerin umarni wanda aka tsara, wanda idan aka aiwatar dashi yakan sanya kwamfuta tayi abin da ake so tayi. Haka zalika computer program jerin umarni ne masu nasaba da juna waɗanda ke baiwa kwamfuta umarnin yadda zata cim ma takamaiman aiki. Wannan dalilin yasa ba tare da program ba kwamfuta ba zata iya aiwatar da komai da komai b Programming: shine aikin rubuta code ko yin aiki domin rubuta computer program. Programmer: shine wanda yake rubuta code ko jerin umarni ga kwamfuta yayin programming. Code (source code): kalma ce wadda ake amfani da ita don bayyana rubutu wanda computer programmer yake rubuta shi ta amfani da dokoki da ƙa'idoji na wani programming language. Coding: wannan shine yin rubutu ko rubuta code. Computer language: shine yaren da kwamfuta take amfani da shi domin fahimtar aikin da aka umarce ta tayi. Programming Language: shin...

Yanda Ake Koyon Programming

  YAYA AKE KOYON PROGRAMMING? A cikin wannan kasida, mun kawo muku wasu matakai da zaku bi domin koyon programming a saukake. Wadannan matakai sune kamar haka: 1. Zabar programming language 2. Farawa da kadan-kadan 3. Yin amfani da code din da wasu programmers din suka rubuta 4. Yawaita shiga dandalin programmers. 1. Zabar Programming language Sau da yawa masu koyon programming sukan rasa ko ma da wane programming language zasu fara. Wannan na faruwa saboda yawan programming languages da muke da su. Kuma a ko da yaushe ka tambayi masana akan wane programming ne yafi dacewa a fara da shi, zaka ji a ko da yaushe amsoshinsu na cin karo da juna. Wani programmer din idan ka tambaye shi sai y ace ka fara da java, a lokacin da wani zaya iya ce maka ka fara da C, shi kuma wani cewa zaya yi ka fara da swift, ko Ruby da dai makamantansu. Maganar gaskiya babu wani programming da za’a dauka a ce shine ya fi kowa ne programming saukin koyo, hasali ma dai, zaka iya fara ...

TSOKACI A KAN YANDA AKE HADA WEBSITE(1)

  Gaba daya website ko kuma shafin internet za'a iya raba shi gida biyu ta la'akari da yanda ake hada shi (wato web design) da kuma abubuwan da ake amfani da su wajen hada shi. Hada website ko kuma web design ya kasu zuwa gida biyu kamar haka: 1. Sashen da ake iya gani idan an ziyarci website din (wato Front-end) 2. Sashen da mutum wanda ya ziyarci website din baya iya gani (wato Back-end) 1. SASHEN DA AKE GANI IDAN AN ZIYARCI WEBSITE(FRONT-END) Shi front-end, ko kuma sashen da ake gani idan an ziyarci website, ya kunshi duk wani dubaru da ake iya amfani da su wajen yin designing ko kuma tsara duk wani abu da ke a cikin website wanda idan mutum ya shiga website din zaya iya gani. Abubuwan da za'a iya gani a cikin website sun hada da hotuna, videos, rubutu, audio da dai sauransu. Ana amfani da abubuwa biyu zuwa uku ne wajen designing din front-end na website.  Na daya, kuma jagora daga cikin wadannan abubwa da ake hada website da su, shine HTML (Hypertext Markup Language). S...