Mutane da yawa, musamman ma masu amfani da manyan wayoyi na zamani, sukan koka akan yanda datarsu ke saurin karewa da zarar sun yi subscription. Wannan dalili ne ya sanya wasu ma kan bar yawan bude datar ko kuma ma su rabu da wayar baki daya. Wannan abu ba hakanan kawai faruwa ba, akwai dalilai da kan sanya hakan. A cikin wannan kasida tamu, zamu yi tsokaci akan wadannan dalilan da kuma yanda zaku shawo kan wannan matsala ta yawan shan data. Sanin kowa dai ne a wannan lokaci da muke a cikin, kusan dukkanin wayoyin da muke amfani da su, musamman ma manya wayoyi, mafi yanwancin aiyukansu sun dogara ne akan internet. Wannan dalili ne ya sanya cewa, idan har mutum baya da data a cikin layinsa, to sai ka ga ya kasa yin wasu da yawa daga cikin muhimman ayyukan da wadannan wayoyin kan yi. Saboda amfanin da wadannan wayoyin ke yi da data ne ya sanya aka basu damar cewa, da zarar mutum ya kunna data, to su ci gaba da yin wasu muhimman...